Posts

Showing posts from March, 2020

Faifain bidiyo yayi wa El-rufai fallasa

Image
Faifain bidiyo yayi wa El-rufai fallasa . Wani faifain bidiyon sirri yayi wa malam Nasir El-rufai tonan asiri, faifain bidiyon da aka dauke sirrance ya nuna yadda El-rufai yake shewa yayin ganawa da wasu mutane. A bayabayan ne bada jimawa ba El-rufai ya bayyana a shafukan sa na sada zumunta cewa", yayi gwajin covid19 sakamako ya fito kuma yana mai bakin cikin bayyana cewa ya kamu, sai ga shi a faifain bidiyon da aka saki yana cewa ", " saifa mutune su dauka da gaskene ." (na kamu). Kuna iya bayyana ra'ayin akan hakan

Alkalaman covid19 sun karu a Naijeriya NCDC

Image
Alkalaman Covid19 sun karu a Naijeriya NCDC A daren jiya 29 ga watan 3 na 2020 ne hukumar NCDC (National Center for Diseases Control) a turance. Hukumar dake lura da yaduwar cutuka ta kasa, a jiya lahadi ta bayyana cewa an samu karuwar wanda suka kamu da cutar ta covid19 wanda aka fi sani da #coronavirus daka tamanin da tara (89) zuwa dari da sha daya (111) yayin da ta bayyana Lagos a jihar da tafi kowacce yawan musu dauke da cutar. Tushe: covid19.ncdc.gov.ng  By ht24n.blogspot.com

An yankewa matar da taiwa dan sanda atishawa hukuncin zaman kidan yari

Image
Kotu ta daure wata mata a gidan yari bayan ta yi wa wani jami'in dan sanda tari a fuskarsa inda ta ke ikirarin cewa tana dauke da kwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da coronavirus. Joanne Turner, mai shekaru 35 da haihuwa ta fara zagin 'dan sandan ne bayan ta lalata wani mota da aka yi pakin a wajen tashar jiragen kasa na birnin Norwich da misalin karfe 11 na daren ranar Laraba. A kotun majistare da ke Norwich a ranar Alhamis, Turner ta amsa cewa ta ci zarafin wani ma'aikacin bayar da gaggawa a cewar 'yan sandan Norflok. Coronavirus: Kotu ta aike da matar da ta yi wa dan sanda tari a fuska gidan yari Ta amsa cewa tana cikin maye kuma ta yi dabi'a na rashin da'a da tayar da hankulan al'umma da lalata kaya kamar yadda New Telegraph ta ruwaito. Rundunar 'yan sanda na Norwich ta ce an yanke wa Turner hukuncin zaman watanni 12 a gidan yari. Dave Marshall ya ce, "Ba za mu amince da wani cin mutunci ko cin zarafi ga jami'an bayar da ta...

Shugaban 'yan Izala zai amsa tambayoyi a gaban jami'an tsaro

Image
Gwanatin jihar filato a najeriya da jami'an tsaro sun gayyaci  shugaban  majalisar malamai na kungiyar izala domin amsa tambayoyi sakamakon karya dokar hana cunkuson jama'a a wuraren ibada. Gwamnatin Jihar Filato  ta mayar da martani game da matakin da shugaban majalisar malamai na Kungiyar Izalar Najeriya Sheik Sani Yahaya Jinigr yayi biyo bayan jagorar Sallar Juma'a  da dandazon mutane fiye da  50 bayan ta dauki matakin hana yin haka a ko ina cikin fadin jihar.  Sakataren gwamnatin jihar Filato Farfesa Danladi Atu ya ce gwamnatin jihar ba za ta amince da karya dokokin da aka kafa domin kare lafiyar al'umma ba sakamakon bullar wannan cuta ta Coronavirus. Cikin martaninsa lokacin taron manema labarai da maraicen yau a Jos fadar gwmanatin ta Filato, sakataren gwamnatin ya ce jami'an tsaro sun gaiyyaci shugaban majalisar malamai na Kungiyar Izalar Sheikh Sani Yahaya Jingir domin ya bayyana dalilansa na jagoratar sallar Juma'a da ...

'Yan Naijeriya sunyi martani akan kyautar maganin Covid19

Image
'Yan Naijeriya sunyi martani akan kyautar maganin Covid19 da wani biluniya yayi masu. Bilunuyan lamba daya dan Kasar China Mr Jack Ma jagoran Gidauniyar AliBaba Group , ya samar wa Naijeriya tarin maganin cutar sarkafewar numfashi ta Corona virus da na'urorin gwada cutar ta Covid19. A jiya da yamma kayan suka iso Naijeriya daka Kasar China, kayan sun kunshi: takunkumi(mask) gud miliyan biyar(5000000) da na'urorin gwaji guda miliyan daya da dubu dari takwas 1.8M da kuma rigunan kariya guda dubu 60000 wanda su daka cikin kayan suka isa Adis-ababa babban birnin Habasha(Ethiopia) a ranar Litinin. Premium times , ta rawaito cewa", yan Naijeriya da dama ne a shafikan sada zumunta suke nuna rashin gamsuwar a kan kyautar gami da zargin cewa kayane da aka riga aka yi amfani dash a China.

Kalaman Gaddafi da na Sadam Hussain akan Covid19

Image
Assalam barka da wannan lokacin fatan alkhairi gare ku. Jawaban da sadam Hussain da kuma Gaddafi suka gabatar akan covid19 kamar sun san haka zata faru, koda yake abun mamaki ne ace Gaddafi ko Sadam Hussain wani a cikin su yayi magana akan covid19. Sadam Hussain a wani faifen bidiyo nashi da aka saki yana tattaunawa da 'yan majalissun sa a shekarar alif 1990 yana bayyana musu cewa", Amurka na yiwa Iraqi barazana da wani virus mai suna Corona, wanda wannan cuta da duk wanda ta kama rayuwa zata tsananta a gareshi. Gaddafi, a bangaren Gaddafi kuma yana cewa" mutanan yammacin duniya(turawa) sun kware wajen kirkirar matsala ga lafiyar dan Adam don samu kudi, batare da tunanin wacce irin matsala zata haifar ba.

Matsayar gwamnatin jihar Kano

Image
Matsayar gwamnatin Kano akan annobar sarkafewar numfashi ta corona virus (covid19) koda yake a baya-bayan nan a kaji cewa", an sami wanda ake zargin ya kamu da cutar sarkafewar numfashi ta corona virus (covid19) gwamnatin jihar Kano ta karyata duk wani jita-jita da ake ya dawa na cewar", a jihar Kano an samu bullar cutar sarkafewar numfashi ta Covid19 gwamnatin ta bayyana hakan ne ta hanyar manyan jami'an lafiya na jihar. Gwamnatin ta bayyana cewa", abun takaici ne yanda wasu marasa kishin kasa(Naijeriya) ke amfani da shafukan CCN da BBC na bogi wajen yada labarai marasa tuhu. A hannu guda kuma gwamnatin ta nemi a rage duk wani taro na cinkoson jama'a.         Hanyar lafiya a bita da shekara. 

Fati Washa ( Tarishin ta Hotunanta) karo na farko

Image
Fatima Abdullahi wadda aka fi sani da Fati Washa shahararriya jarimar wadda ake kira da Fati Washa, an haife ta a 21 ga watan febrairu(February) na shekarar alif 1993 a jihar Bauchi . Ana kiranta da Tara Washa ko Washa kawai. Fati Washa nad shekara 27 kuma tana zaune ita kadai (ba aure) Fati Washa na daya daka cikin kyawawan jaruman masana'antar shirya fina finan Hausa ta Kanywood ; tarishin ta a baya a 6oye yake amma wani sahi na tarishin ya bayyana, Fati Washa kyakkyawace, mai hazaka, mai yawan fara'a kuma jarumace mafi tsada a masana'antar Kanywood, wanda hakan ya bawa magoya bayanta damar kirkirar shafukan sada zumunta na goyon baya. Washa ta yi gagarumar nasara a masana'antar Kanywood . Kashi na daya na tarishin nata ya kammala ku cigaba da bibiyar mu don kawo muku kashi na 2 da na uku.  

Muna son aure suna tsoro

Image
Aisha Abdullahi daliba a Jami'ar maitama dake Kano dalibar wacce take a shekarar ta 4 a sahin nazarin sassan jikin halitta da sunadarai (Biochemistry) ta bayyana cewa mafi yawan 'yan matan makaranta na son suyi aure, amma 'yan samari na tsoron kulasu sabida tsoron kalmar da ake fada musu. Aisha ta bayyana hakan a yayin wata lakca da aka shirya ma daliban makaranta mai taken;     Kalubalen aure a karni na ashirin da daya(21st). Ta bayyana cewa ",mafi yawan matasa na fadawa soyayya da 'yan mata, da sun yi musu maganar aure sai mazan su gudu ba dan kuma suna da aure ba, ta bada musali da wani da suka kwashe shekara 2 suna soyayya amma da akai mai maganar aure sai ya there. Ta kuma zargi rashin kamun kai a abunda yake yawan haifar da mutuwar aure. A karshe an tambaye ta shin tana son aure in ta kammala karatun ta, sai ta ce "ko na samu wanda ya shirya aurena bazan amunce ba." Opera News cikin harshen Turanci.

Dalilin da yasa naki aurar Dangote Nafisat

Image
Ba abunda yasa naki aurar Dangote sai dan kasancewa ta kawar 'yarsa . Naijeriya in har hana maganar sana'o'i/ kasuwanci baza a manta da Aliko Dangote ba. Aliko Dangote ya auri mata uku, kuma duk yarabu da su. Aliko Dangote ya auri matarsa ta fari a shekarar alif 1977 amma auren bai dade ba ya mutu, da ka karshe Aliko Dangote ya nemi auren yar tsohon shugaban kasar Naijeriya  Umar Musa Yar Aduwa. Don ya maye gurbin matar sa ta fari, tsohon shugaban kasar nada y'a'ya mata uku, wanda suka hadar da: Nafisat, Maryam da Zainab Yar aduwa. Nafisat 'yar aduwa itace, wanda Dangote ya nemi auren ta a shekarar 2009 amma taki amincewa, ta bayyana cewa taki amincewa ne sabida ta kasancewarta kawa ga yarshi Halima Dangote. Nafisat 'Yar aduwa a karshe dai ta auri tsohon gwamnan Bauchi, sauran 'ya'yan Yar aduwa duk sun auri tsofaffin gwamnoninin wash jahohin. Nafisat nada yara 4 guda uku maza guda daya kuma mace.              

Yan kwallon kwafa guda 10 ne suka sauya addini

Image
Yan kwallon kwafa guda goma ne suka sauya addini. Yayinda guda takwsa daka goman duk suka sauya daka addinin nasaranci(Christianity) zuwa addinin Musulunci, guda biyu kuma daka ciki a iya cewa", abun dacene ko rashin dacene? Koda yake akwai manufofi da dalilai daban daban da suke sa mutane sauya ra'ayin su, zamuji abunda yasa su sukai hakan; ga jerin sunayen su nan da dalilan su: 10. Franck Ribery ( Nasaranci zuwa Musulunci) Franck Ribery ya taka leda na tsawon shekaru 12 a kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich's kuma ya ci mata kwallaye 16. Franck Ribery ya muslunta a shekarar 2002, bayan aurensa da matar sa Wahiba yar asalin Algeria (Aljeriya), ya muslunta kuma ya sauya sunan sa zuwa bilal an rawaito yana cewa", "addini yana daka abunda na dauka da muhimmanci, kuma yanzu na zama mai zama mai imani, na zama mai karfin tinani, karfin hankali game da karfin guwa." 9. George Weah (Nasaranci zuwa Musulunci zuwa Nasaranci) George Wheah ya rayu ya...

'Yar shekara 62 ta auri dan shekara 9

Image
Barka da wannan lokaci fatan alkhairi ga musu bibiyar wannan shafin. Turkashi, ashe ba a jihar kano bane a ka fara mace ta aure wanda ta girmawa sosai ba, sai dai a jihar kano a iya cewa" abun ba wai maganar shekaru bace kadai a kwai maganar cewa" ba 'yar kasa bace bayan fifikon shekaru. A Kasar South Africa,(Afurka ta kudu) abun yafi ban al'ajabi yayin da 'yar shekara sittin da biyu (62) ta aure dan shekara tara(9). Dattijuwar yar shekara 62 da ta auri dan shekara 9 a shekarar 2014 bayan rasuwar mijinja a shekarar 2013 na dauke da juna biyu, matar mai suna Lungile Kumasi ta aure yaron mai suna Khabonina Khabo, wanda ta bawa kakar shi ta bangar en mahaifiyar sa shekara 4, koda yake a al'adar Afurka ta kudu ta aure yaron ne don ya maye gurbin rushin tsohon mijinta, bayan shekaru 4 da yin auren su yaron yayi nasarar kasancewar matarsa mai juna biyu, kuma yana gab da zama uba wanda a halin da ake ciki yana da kimanin shekara 13 matar kuma nada shekara 66. ...

'Yar shekara 62 ta auri dan shekara 9

Barka da wannan lokaci fatan alkhairi ga musu bibiyar wannan shafin. Turkashi, ashe ba a jihar kano bane a ka fara mace ta aure wanda ta girmawa sosai ba, sai dai a jihar kano a iya cewa" abun ba wai maganar shekaru bace kadai a kwai maganar cewa" ba 'yar kasa bace bayan fifikon shekaru. A Kasar South Africa,(Afurka ta kudu) abun yafi ban al'ajabi yayin da 'yar shekara sittin da biyu (62) ta aure dan shekara tara(9). Dattijuwar yar shekara 62 da ta auri dan shekara 9 a shekarar 2014 bayan rasuwar mijinja a shekarar 2013 na dauke da juna biyu, matar mai suna Lungile Kumasi ta aure yaron mai suna Khabonina Khabo, wanda ta bawa kakar shi ta bargen mahaifiyar sa shekara 4, koda yake a al'adar Afurka ta kudu ta aure yaron ne don ya maye gurbin rushin tsohon mijinta, bayan shekaru 4 da yin auren su yaron yayi nasarar kasancewar matarsa mai juna biyu, kuma yana gab da zama uba wanda a halin da ake ciki yana da kimanin shekara 13 matar kuma nada shekara 66. Karshe...

An gano maganin cutar CoronaVirus

Image
Barka da wannan lokacin kuma tare da sahin labarai na Hausa Time  An gano maganin cutar corona virus A can kasar sin wato China kamar yadda daka nan a ka fara samo cutar ta corona virus to fa a can-ne a ka fara gano maninta, yayin da asibitin kasar sin wanda wata majiya take nuna cewa", a kwana goma (10) aka gina asibitin kuma an ginashi ne musamman don kula da wadanda suna kamu da cutar ta corona virus, asibitin ya sallami kiminan mutum dubu daya da dari biyar (1500) da suka warke daka cutar ta corona virus, bayan ada baya an same su da cutar ta corona virus (COVID19). China (sin) a can a ka fara samun barkewar cutar ta corona virus, to a canne fa a ka fara gano maganinta.

Kamfanin Google na aikin samar da manhajar gwada Corona virus

Image
Assalam barka iwar haka, da fatan zaku cigaba da kasancewa damu .  Kamfanin Google ya bayyana cewar" zai samar da wata manhaja da za a ringa amfani da ita wajen gwaji don gano cutar corona virus [Korona bairos(COVID19)]. Shugaban kasar Amurka Donal Trumph, ya bayyana a shafinsa na twitter (tiwita) cewar kamfanin Google na aikin samar da manhajar da za a ringa amfani da ita don gano cutar corona virus, koda yake tun kafin shugaban na Amurka Donal Trumph ya bayyana haka kamfanin na Google ya bayyana cewar " daman yana akin samar da manhajar. Kamfanin Google din a halin yanzu haka ya bayyana cewar" yana gab da kammala aikin samar da manhajar wacce zata bawa mutune damar yi ma kanso gwaji don gano cewar ko suna dauke da cutar ta corona virus ko sabanin haka.

Hardworking platform [hwpform]

Image
HARDWORKING PLATFORM Cordially invite you to special meeting it prepared.   Scheduled to take place as follow: Day:Saturday 14 March 2020  Time:9am Venue coral spring academy, old table water (klin)company. About us: Hardworking platform, is a part of DDIG that is now going to be  refund, customize, and renamed by the leaders of DDIG . Motto: let's enlight and build our future together. Our Mission: is to educate one another, to provide good and quality job to our members.   Who ever the invitation card reached, he should have to attend. Thanks                           Signed by                       Secretary & Special Advisor The mentioned people below are really invited: Sir Abdullahi Maikano Sir Abubakar Soldier Sir Abubakar Engineer Sir Abubakar Yellow Sir  Abdullahi Soja Sir Habib Alai Sir Ibrahim Ya hajid Si...