An yankewa matar da taiwa dan sanda atishawa hukuncin zaman kidan yari
Kotu ta daure wata mata a gidan yari bayan ta yi wa wani jami'in dan sanda tari a fuskarsa inda ta ke ikirarin cewa tana dauke da kwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da coronavirus.
Joanne Turner, mai shekaru 35 da haihuwa ta fara zagin 'dan sandan ne bayan ta lalata wani mota da aka yi pakin a wajen tashar jiragen kasa na birnin Norwich da misalin karfe 11 na daren ranar Laraba.
A kotun majistare da ke Norwich a ranar Alhamis, Turner ta amsa cewa ta ci zarafin wani ma'aikacin bayar da gaggawa a cewar 'yan sandan Norflok.
Coronavirus: Kotu ta aike da matar da ta yi wa dan sanda tari a fuska gidan yari
Ta amsa cewa tana cikin maye kuma ta yi dabi'a na rashin da'a da tayar da hankulan al'umma da lalata kaya kamar yadda New Telegraph ta ruwaito.
Rundunar 'yan sanda na Norwich ta ce an yanke wa Turner hukuncin zaman watanni 12 a gidan yari.
Dave Marshall ya ce, "Ba za mu amince da wani cin mutunci ko cin zarafi ga jami'an bayar da taimakon gaggawa a kowanne lokaci. Wannnan hukuncin da aka yanke ya nuna munin yi wa mutane tari a fuska ko kuma razana mutane game da yaduwar da Covid-19."
Rundunar 'yan sandan ta kara da cewa wannan hukuncin dakotu ta yanke zai zama gargadi ga duk wanda ke tunanin aikata laifi irin wannan na yi wa mutane barazana ko razana su yayin wannan lokacin annobar.

Comments
Post a Comment
Please leave your comment here