Shugaban 'yan Izala zai amsa tambayoyi a gaban jami'an tsaro
Gwanatin jihar filato a najeriya da jami'an tsaro sun gayyaci shugaban majalisar malamai na kungiyar izala domin amsa tambayoyi sakamakon karya dokar hana cunkuson jama'a a wuraren ibada.
Gwamnatin Jihar Filato ta mayar da martani game da matakin da shugaban majalisar malamai na Kungiyar Izalar Najeriya Sheik Sani Yahaya Jinigr yayi biyo bayan jagorar Sallar Juma'a da dandazon mutane fiye da 50 bayan ta dauki matakin hana yin haka a ko ina cikin fadin jihar.
Sakataren gwamnatin jihar Filato Farfesa Danladi Atu ya ce gwamnatin jihar ba za ta amince da karya dokokin da aka kafa domin kare lafiyar al'umma ba sakamakon bullar wannan cuta ta Coronavirus.
Cikin martaninsa lokacin taron manema labarai da maraicen yau a Jos fadar gwmanatin ta Filato, sakataren gwamnatin ya ce jami'an tsaro sun gaiyyaci shugaban majalisar malamai na Kungiyar Izalar Sheikh Sani Yahaya Jingir domin ya bayyana dalilansa na jagoratar sallar Juma'a da mutane fiye da 50, kamar yadda doka ta amince a yi.
Kawo yanzu dai babu wasu cikkakun bayanai daga bangaren jami'an tsaro kan matakin gaiyyatar malamin don amsa tambayoyin.
Comments
Post a Comment
Please leave your comment here