Kamfanin Google na aikin samar da manhajar gwada Corona virus

Assalam barka iwar haka, da fatan zaku cigaba da kasancewa damu.
 Kamfanin Google ya bayyana cewar" zai samar da wata manhaja da za a ringa amfani da ita wajen gwaji don gano cutar corona virus [Korona bairos(COVID19)].
Shugaban kasar Amurka Donal Trumph, ya bayyana a shafinsa na twitter (tiwita) cewar kamfanin Google na aikin samar da manhajar da za a ringa amfani da ita don gano cutar corona virus, koda yake tun kafin shugaban na Amurka Donal Trumph ya bayyana haka kamfanin na Google ya bayyana cewar " daman yana akin samar da manhajar.
Kamfanin Google din a halin yanzu haka ya bayyana cewar" yana gab da kammala aikin samar da manhajar wacce zata bawa mutune damar yi ma kanso gwaji don gano cewar ko suna dauke da cutar ta corona virus ko sabanin haka.

Comments