'Yan Naijeriya sunyi martani akan kyautar maganin Covid19

'Yan Naijeriya sunyi martani akan kyautar maganin Covid19 da wani biluniya yayi masu.
Bilunuyan lamba daya dan Kasar China Mr Jack Ma jagoran Gidauniyar AliBaba Group, ya samar wa Naijeriya tarin maganin cutar sarkafewar numfashi ta Corona virus da na'urorin gwada cutar ta Covid19.
A jiya da yamma kayan suka iso Naijeriya daka Kasar China, kayan sun kunshi: takunkumi(mask) gud miliyan biyar(5000000) da na'urorin gwaji guda miliyan daya da dubu dari takwas 1.8M da kuma rigunan kariya guda dubu 60000 wanda su daka cikin kayan suka isa Adis-ababa babban birnin Habasha(Ethiopia) a ranar Litinin.
Premium times, ta rawaito cewa", yan Naijeriya da dama ne a shafikan sada zumunta suke nuna rashin gamsuwar a kan kyautar gami da zargin cewa kayane da aka riga aka yi amfani dash a China.

Comments