Hukumar kula da Lafiya ta duniya ta bayyana wa'adin Covid19

Hukumar kula da lafiya ta duniya wacce aka fi sani da WHO(World Health Organization) a turance, ta bayyana wa'adin cutar sarkafewar numfashi ta coronavirus wato Covid19. Wani rahoto da gidan telebijin na Aljazeera ya fitar a yau 16/4/2020 ya bayyana cewa hukumar kula da lafiya ta duniya ta yi ikrarin cewa cutar annobar sarkafewar numfashi ta coronavirus wato Covid19 za ta iya kaiwa shekarar 2024 a fad'in duniya wanda hakan na nufin za ta iya kaiwa tsawon shekaru  hud'u kafin a samar da ingantaccen   maganinta da zai aiki a kan ta, don ba cuta ce irin sauran cututtuka ba, wannan cutar ta na barazana ne ga duniya gabad'ya  dangane da tattalin arzuki lafiyar jam'a.
Rahoton Aljazeera

Comments