Zuwan Musulunci kasar Hausa

Zuwan Musulunci kasar
Ka marya yadda masanin Hausa kuma kwararen marubucin Hausa Dr Danjuma  Sani yabayyana a littafin Gishirin zaman duniya na (4)
Shi dai addinin Musulunci (Islam) addini ne wanda Allah ya aiko annabi Muhammadu dashi. Annabi Muhammad (S.A.W) Balarabe ne. An haife shi a Makkah wadda take a kasar saudiya a yanzu.
Addinin Musulunci yafara yaduwa cikin duniya ne a karni na bakwai. Tun wannan lokaci ne kuma yazo Afurka, musamman misra. Wannan addini ya yi ta yaduwa kamar wutar daji cikin Afurka inda al'umomi da yawa suna rungume shi.
Addinin Musulunci ana kyautata zaton yazo ya kuma kankama a kasar Hausa ne a karni na sha daya. Wannan addini ya zo kasar Hausa ta hanyoyi biyu. Hanya ta farko itace ta dalilin kasuwanci dake tsakanin Hausawa da mutanen Afurka ta Arewa(Maghreb) su mutanen Afurka ta Arewa sun dade da karbar Musulunci. Don haka ta dalilin kasuwanci sun yada addinin ga ‘yan kasuwa Hausawa.
Hanya tabiyu da addini ya bi ya shigo kasar Hausa itace ta dalilin zuwan masu wa'azi. Na farko irin wandannan mutane sune wangarawa. Aance sun zone a karni na sha hudu  karkashin shugabancin wani shahararren malami Shehu Abdurrahman Zaite saga kasar Mali. Shi dai mutanensa sun bazu kasar Hausa India suka dinga wa'azi suna shigar da mutanen cikin addinin Musulunci. Sun giggina masallatai da yawa. Duk inda suna je, sukan fara musulutar da sarkin wurin ne. A Karni sun zo zamanin sarki yaji dan tsamiya. Wash shahararrun malaman ma sun zo kasar Hausa bays ga wangarawa. Wani fitacce cikinsu shi ne shaik Muhammad bn Abdulkarim Al-Maghili. Wannan malami ya zo ne zamanin sarkin Kano Muhammad Rumfa  wanda yayi sarauta daga 1463 zuwa 1499. A wannan lokaci ne aka sare bishiyar nan Tsinburbura wanda ake bautar tsafi da bautar tsafi a wurita. Wannan ya kara karfafa Musulunci a zukatan mutane, ya kuma kawar da addinin gargajiya a tsafi da bautar aljanu.
Sannu a hankali kafin kace kwabo, Musulunci ya yadu kasar Hausa ko'ina da ko'ina. Akasarin Hausawa  suka musulunta, addinin Musulunci kuma ya zama addinin kasa wanda ake hukunci da shari'ar sa. Masana  sunce fiye da kashi 90 cikin 100 na Hausawa musulmai ne.  

Comments