An kashe dakarun ƴan sanda guda biyu a masana'antar Atiku Abubakar

An kashe dakarun ƴan sanda guda biyu a masana'antar Atiku Abubakar
An samu rahoton cewa an kashe yan sanda guda biyu a wata masana'antar harkokin dabbo wacce take mallakin tsohon mataimakin  shugaban ƙasan Naijeriya Mlm Atiku Abubakar
Yan sandan guda biyu an kashe su yayin da suke gudanar da bincike a masana'antar abuncin dabbobi ta RicoGado dake jihar Adamawa mallakin tsohon mataimakin shugaban, yan sandan sun haɗar da ASP Yohana da kuma DSP Gbenga; mai magana da yawun ƴan sanda ya tabbatar da faruwar hakan ga jaridar Sahara, sai dai kuma mai magana da yawun Atiku Abubakar ya musanta hakan ga jaridar Politics Nigeria (Siyasar Naijeriya)
Jaridar Politics Nigeria ce ta rawaito hakan cikin harshen Turanci.

Comments