Banbancin Hausa dakuma Hausawa

Banbancin Hausa dakuma Hausawa.

             Barka da wannan lokaci tare da Hausa TimeTime.
Kusan abune sananne a wajen al'umar Hausa idan akace Hausa ana nufin yaren Hausa ko yaren kasar Hausa. Yaren Hausa yanzu haka yana daya daka manya-manyan harshinan kasuwanci, da sadarwa na Afurka ta yamma kai a yanzu haka harshen Hausa ya hau sahun shahararrun harshinan duniya, harshen/yaren kasar Hausa yarene da yafi karfi a arewacin Nigeria fiye da ko ina a duniya. Buncike ya nuna cewa kimanin akalla mutum miliyan hamsin ne (50M)suke magana da harshen Hausa.harshen Hausa harshene da ake karantar dashi yau a manya-manyan jami'o'in duniya da sannan a Nigeria ana karantar dashi a duk jami'o'in kasar; kai har ilah yau harshen Hausa ya samu tagomashin kasancewa daya daka harshinan yada labarai a manyan kafofin yada labarai na duniya kamar su: BBC dake da babbar cibiya a Burtaniya(England) . VOA dake da babbar cibiya a'Amurka. DW jamus dake da babbar cibiya a Jamani. Da kuma FRI dake da babbar cibiya a Faransa. Harshen Hausa bai tsaya anan ba amma zaku ji karin bayanin a cikin ma'anar su wane Hausawa.
Hausawa~
Hausawa sune mutanen arewacin Nigeria da kuma wani yanki na kudancin Niger (nijar) mutanene dake da al'adu da ban da ban, sannan a karan kansu al'adun wannan garin da na waccen garin sun saba duk dacewa", ba wani sabanine mai yawa ba. Al'umar Hausa a yanzu haka suna rubutun litattafai na karatu da wakoki dakuma wasannin kwai-kwayo. Jihar Kano dake  arewacin Nigeria kuma cibiyar kasuwancin Nigeria ita akewa kallon matsayin babbar cibiyar  Hausa ta duniya duk dacewa", ana mata kallon ba itace  tushen Hausa ba duk da ganin cewa Hausawan jihar kano sune, akewa kallon hausar su tafi kama da daidaitacciyar Hausa.
Sai kucigaba da bibiyar mu don kawo muku tarshin kasar Hausa.  

Comments